11 Nuwamba 2020 - 11:26
Sojojin Kasar Rasha Sun Isa Yankin Nagorno-Karabakh Don Tabbatar Da Zaman Lafiya

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bada sanarwan cewa sojojin kasarsa sun fara isa yankin Nagorno-Karabakh, inda kasashen Azerbajan da Armenia suke takaddama kan mallakarsa tun watan Satumban da ya gabata.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar tsaron kasar Rasha tana fadar haka a yau Talata, ta kuma kara da cewa, a yau ne kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen yaki tsakaninsu. Sannan tuni sojojin tabbatar da zaman lafiya a kan iyakokin kasashen biyu 1,960 suka isa yankin.

Yankin Nagorno-Karabakh dai na kasar Azerbajan ne, amma bayan wargajewar tarayyar Soviet a shekara 1991, kasar Armenia ta ingiza ‘yan kabilar armeniyawa mazauna yankin na Nagorno-Karabakh, suka balle daga kasar Azerbajan a shekara ta 1992, bayan an kashe mutane kimani 30,000, a tsakanin yan tawaye Armeniyawa da kuma sojojin kasar Azerbajan.

A bisa dokokin kasa da kasa dai yankin Nagorno-Karabakh mallakin kasar Azerbajan ne, amma ‘yan kabilar Armani ne suke zama a yankin. Don haka yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla a yau Talata, ta bukaci gwamnatin kasar Armeniya ta mika wasu karin yankunan da suke karkashin ikonta ga kasar Azerbajan, daga yanzu zuwa daya ga watan Decemba mai zuwa.

342/